<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>28</hymn_number>
<title>Ku, Za Ku Ina? LW28</title>
<lyrics>[V1]
 Ku, za ku ina?
 Za mu tafi majami'a, mu yi wa Allah yabo.
 Yabon menene?
 Domin abinci, rai da sutura da Allah ya ke ba mu.
 Wannan kaɗai, ko?
 A'a, daa sauran abu da yawa da Allah ya ke ba mu,
 Sauran menene?
 Saura dayawa, kwanciyar zuciya,
 Murna da farinciki
 Don me da murna?
 Muna murna saboda Yesu ya zo ya kawo ceto.
 Kuna biya menene?
 Ba mu biya ba, daga alherinsa ya biya laifofinmu.
 Ƙaƙa zan samu?
 Tuba ka yarda Allah ya aiko Yesu
 don ya ceci duniya
 Wannan na yarda.
 To, ya isa, an cece ka, ka zo mu tafi tare.
 Za ni tare.
 To mu tafi majami'a mu yi wa Allah yabo.</lyrics>
<author>Donnie Sax Sanders &amp; the Loud Cry Revival</author>
</song>